1
A ranar 26 ga watan Disamban 2026, Isra’ila ta sanar da amincewa da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta, duk da cewa wannan yankin tsawon shekaru fiye da talatin yana neman ballewa amma kasashen duniya ba su amince da shi a matsayin kasa ba.
2
Ya kamata mu dan yi dubi kan matsayin yankin Somaliland, yankin da ya hada Mediterrenian, gabas ta tsakiya da kuma tekun India.
3
Bayan farmakin Guguwar Al’aqsa, Isra’ila ta yunkuro domin fadada kutsenta a kahon Afirka da Red Sea da sunan bunkasa diflomasiyya.
4
Wannan yana da alaka ne kai tsaye da damuwar da take da ita kan bangarorin da ke kawance da Iran kamar Ansarullah na kasar Yemen.
5
Kulla alaka da Somaliland zai iya ba Isra’ila damar kafa wuraren leken asiri da na tsaro a kusa da Yemen, wurin da daga nan ne makamai masu linzami da jirage marasa matuka na ‘yan Huthi suke wucewa.
6
Ta fuskacin hanyoyi kuwa, Somaliland tana a wani wuri ne wanda ya hada hanyoyin ruwa na duniya, wanda za a iya yin amfani shi wajen shimfida iko a kan harkokin zirga-zirga a cikin ruwa.
7
A kan haka, wannan zai iya zama lamari ne da aka tsara domin samun damar isa da kuma sanya ido a kan wuri mai matukar muhimmanci,
8
Lamarin da maimakon ya tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin, zai kara habaka ayyukan leken asiri da tsaro na Israi’ila ne kawai.
9
Ta fuskar fashin baki kuwa, wannan lamarin yana nuni ne da yunkurin yin kutse ta hanyar halasta wani abu da ke tattare da alamar tambaya, da kuma yin amfani da raunin iko a Afirka.
10
Wannan siyasar ba wai kawai tana raunana hakkoki na kasa da kasa ba ne, har ma hakan yana mayar da yankuna masu rauni su zama wuraren gasa, da kuma haifar da matsaloli da rashin tsaro a yankin Red Sea, da kuma shimfida hanyar fadada rikice-rikice.
11
Ta hanyar halasta haramtacciyar gwamnati, Isra’ila tana son fadada ayyukan sa ido a kan ‘yan Huthi, da kuma sufurin jiragen ruwa.
12
Amma wannan dabi’a ta son kai ta Isra’ila tana tattare da wasu munanan abubuwa ga Afirka, za mu iya yin nuni da wasu daga ciki:
13
1 Haifar da Rashin zaman lafiya da karuwar rikice-rikice
2 Tunzura kungiyoyin ‘yan aware a cikin sauran kasashe
3 Zai zama silar sabon rikici a yankin
4 Karuwar tsoma bakin kasashen waje da sabani na diflomasiyya
5 Bulluwar matsaloli na jin kai da kuma tilasta mutane yin hijira