1
Mun sha jin labarai da bayanai akan yadda ake tsarin iyali, da yadda ake da sa ido akan hajar da aka kera, domin tantance nagartarsu, da kuma kula da zirga-zirgar motoci.
To ko za ku yarda da cewa ‘yan sahayoniya suna da wani tsari da shiri akan bayanan da za su shigar da shi a cikin kwakwalen mutane danagne da tarihi?
2
A wannan lokacin da akwai wata cibiya ta duniya wacce ta kunshi kananan cibiyoyi na al’adu, kafafen watsa labaru, da cibiyoyin koyarwa da suka hadu suna aiki akan tarihin yahudawa; Ga misali da akwai cibiyar “ USC Shoa Foundation.”
3
Wannan cibiyar, ta fitar da fina-finan da sun kai dubu 55 akan riwayar da su ka kitsa akan kisan kiyashin yahudawa na “Holocaust” , an kuma watsa su a cikin kasashe 65 a cikin harsuna 43.
4
Ko kuma cibiyar “National Centre For Jewish Film” wacce take da rumbun adana fina-finai, ta yi wa wasu fina-finan kwaskwarima da kuma yin wasu sabbi akan yahudawa da sun kai 30,000. Ita ce take ayyana wadanne hotuna ne na tarihin yahudawa za a kare da kiyaye su, sannan kuma wadanne ne za a yi amfani da su a koyarwa a cikin jami’o’i.
5
A wani sabon mataki, cibiyar “OpenDor Media” ta yi gajerun fina-finai da dogayen fina-finai na tarihi da miliyoyin shafukan internet suke dauka daga wurinsu, kuma sun yi su ne a cikin harshe mai sauki saboda samari da matasa.
6
Wannan yana nufin samar da wata Babbar cibiya da za a rika komawa gare ta domin koyar da tarihi a fadin duniya.
7
Haduwar wadannan cibiyoyin uku da yin aiki akan tafarki daya, wato , adana bayanai, yin sabbin fina-finai da rabawa, sakamakon da zai haifar ba ya nufin koyar da hakikanin abinda ya faru a tarihi, yana nufin cusa abinda suke so a cikin kwakwalen mutane.
8
A cikin wadannan riwayoyin da akwai abubuwa guda uku da suke maimaita kawukansu; Yahudawa sun sha wahala a tarihi, Sun rayu cikin bakunta da rashin tsaro, sai bukatuwa da samun inda za su rayu a cikin aminci da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
9
Haduwar wadannan abubuwan da ake cusawa a cikin kwakwalwar mai kallo,zai kai ga cimma sakamakon da zai zauna a kansa cewa; Lallai dole ne “Isra’ila” ta cigaba da wanzuwa a matsayin wani abu da ya zama wajibi.
10
A wani gefen kuwa;masu mayar da martani akan wannan Shirin suna cewa; Acikin kasashen turai, ba a barin a bayyana wahalhalun da Falasdinawa suke ciki, saboda za a dauke shi a matsayin kin jinin Yahudawa.Babu daidaito wajen nuna halin da Falasdinawa suke ciki, idan ma ana yi to kadan ne. To shi kanshi rashin bayar da damar nuna halin da Falasdinawa suke ciki daidai wa daida, wani bangare ne na sarrafa abinda ake son ya shiga cikin tunanin mutane.
11
Don haka batun da ake magana akansa anan ba wai “ Wane abu ne gaskiya ba” ana magana ne akan su wanene ke iya ayyana riwayar da za a gani da yawa, da kuma wacce za a gani kadan.