Rasha Zata Kara Kyautata Dangantaka BRICS don Magance Takunkuman Amurka A Kanta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kasar Rasha tana shirin kara dankon zumunci da kungiyar Brics saboda fuskantar takunkuman tattalin arziki wadanda

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kasar Rasha tana shirin kara dankon zumunci da kungiyar Brics saboda fuskantar takunkuman tattalin arziki wadanda kasar Amurka ta daura mata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Maria Zakharova kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka, ta kuma kara da cewa, kungiyar BRICS kungiya ce wace kasar Rasha ta dogara da ita don magance irin wadannan matsaloli. Sannan kasashen iya magance takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suke dorawa kasar Rasha.

Zakharova, ta kara da cewa kasashen Global south da BRICS sune kawayen Rasha a kan abinda ya mshafi matsalolin takunkuman tattalin arziki da kuma kawayenta a cikin harkokin siyasar duniya.

Zakharova ta kara da cewa “Kudaden fito wadanda Amurka take  dorawa kasashen duniya musamman kasashen Global South yana tauye kasancewarsu kasashen masu yenci kuma kokari ne na shishigi a cikin harkokin gida na wadannan kasashe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted