Rasha Tace Shigowar Amurka Yankin Qafqaas Shi Zai Zama Masomin Tashe Tashen Hankula A Yankin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mariya Zakharova ta bayyana cewa Atisayen hadin Giwa tsakanin Amurka da Armenia wanda suka sanya masa suna (Eagle Patner

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mariya Zakharova ta bayyana cewa Atisayen hadin Giwa tsakanin Amurka da Armenia wanda suka sanya masa suna (Eagle Patner 2024) ba abinda zai haifar a yankin Qafqaas in banda fitina a tsakanin kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labaran Tass na kasar Rasha ya nakalto Zakharova tana fada kafin kan kan cewa, atisayen sojan da kasashen biyu suke gudanarwa zai koma kansu ne kawai, don Amurka ta tursasawa kasar Armenia ta fita daga kungiyar kawancen tsaro na yankin, sannan daga baya ta fara sukar kungiyar.

Ta kuma kammala da cewa shigar Amurka a cikin al-amuran tsaron kasar Armenia zai dulmuyata cikin aiki da kungiyar tsaro ta NATO wacce kuma zata yi aiki nan gaba don haddasa matsaloli a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments