Kasar Rasha ta fara tura iskar gasa zuwa kasar Iran ta kasar Azarbaijan, wanda daga karshe zai shiga kasuwan ga kasar ta rasah.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar ta na fadar haka a yau Asabar.
Labarin ya kara da cewa tun taron kwamin hadin guiwa na kasuwanci da tattalin arziki na kasashen biyu ya gudanar da taronsa na hadin guiwa karo na 18 a birnin Mosco, Rasha ta bada sanarwan fara tura iskar gas zuwa kasar ta Iran ta kasar Azirbajan, wanda kuma hakan zai zama kasuwa ga kasar Rasha amma a kasar Iran..
Kasashen biyu dai sun dade suna kokarin karfafa dangantaka a tsakaninsu, musamman bayan da kasashen yamma suka dora masu takunkuman tattalin arziki masu tsananin, saboda yakin da Rasha take yi a Ukraine da kuma saboda shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya.