Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a wani taron sirri da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan mako kasar Rasha ta yi Allah-wadai da sabuwar gwamnatin kasar ta Syria dangane da kisan kiyashin da jami’anta suke yi a kan tsiraru a kasar.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Syria (SOHR) ta sanar da kashe fararen hula 1,383, galibi ‘yan Alawite a cikin makon da suka gabata. SOHR ta ce yawancin wadanda aka kashe fararen hula ne, kuma jami’an da ke da alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne suka kashe su.
Kasar Rasha ta yi gargadi kan karuwar ta’addanci a kasar Syria tare da kwatanta kashe-kashen da kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda da abin da yake faruwa a yanzu a kasar Syria. Ta yadda masu rike da madafun iko da ‘yan bindigar da ke karkashinsu suke tara daruruwan fararen hula daga bangaren marasa rinjaye su kashe su baki daya, kamar yadda ‘yan kabilar Hutu suka rika yi wa ‘yan kabilar Tutsi a Rwanda a shekara ta 1994.
Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia, ya ce abin takaici shi ne babu wata kasa a duniya da ta dauki wani mataki domin ganin dakatar da wannan kisan kiyashi da ake yi a Syria.
Hotunan bidiyo da dama sun nuna Kungiyoyin da ke dauke da makamai karkashin inuwar kungiyar Tahrir Sham mai alaka da alkaida wadda kuma itace ta kfa gwamnatia halin yanzu a Syria tare da taimakon Turkiya da Qatar, su ne suke aiwatar da wannan kisan kiyashi a kan ‘yan alawiyya, bisa hujjar cewa suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Bashar Assad.