Rasha Ta Bukaci Kamfanin Dillancin Labaran Reuters Ya Gyara Kuskurensa Na Bada Labarin Mutuwar Shugaba Asad

Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci kamfanin dillancin labaran Reuters ta gyara labarinsa dangane yiyuwar mutuwar tsohon shugaban kasar Siriya a wani hatsarin jirgen saman da

Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci kamfanin dillancin labaran Reuters ta gyara labarinsa dangane yiyuwar mutuwar tsohon shugaban kasar Siriya a wani hatsarin jirgen saman da yake dauke da shi bayan ya fice daga kasar a jiya Lahadi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Maria Zakharova kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta na fadar haka a jiya Lahadi, ta kuma kara da cewa shugaba Asad bai yi hatsari da jirgin da yake dauke da shi da iyalansa zuwa birnin Mosco ba.

Kafin haka dai kamfanin dillancin labaran rueters dai ya bada labarin cewa mai yuwa shugaba Bashar Al-Asad ya mutu a hatsarun jirgin sama bayan ya fice daga kasar, a lokacin da kungiyar yan tawaye, ta Hai’atu Tahrirusham ta fara shigowa birnin Damascus babban birnin kasar.

Na’urorin sadarwa ta ‘Rada” na jiragen sama, sun nuna jirgin da ya dauki shugaban ya tashi daga wani barikin sojojin kasar Rasha a birnin Damascus, sannan ya nufi Tekun madeterenin kafin a ganshi ya juya baya sannan ya bace daga ‘Radar”.

Daga karshe Maria Zakharova tace: labarinda kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa ya sa mafi yawan kamfanonin labarai suka dauka kan cewa Bashar Al-Asad ya mutu a hatsatin jirgin sama.

Shugaban kasar Siriya da iyalansa dai sun isa birnin Mosco a jiya Lahadi lafiya inda suka sami mafaka daga gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments