Rasha: Sojojin Rasha Sun Kakkabo Jiragen Yakin Ukraine 22 A Daren Jiya

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bada sanarwa a safiyar yau Asabar kan cewa garkuwan sararin samania na kasar sun kakkabo jiragen yakin kasar Ukraine wadanda

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bada sanarwa a safiyar yau Asabar kan cewa garkuwan sararin samania na kasar sun kakkabo jiragen yakin kasar Ukraine wadanda ake sarrafasu daga nesa har 22 a kan wasu yankuna a kasar.

Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto ma’aikatar na cewa sojojinta sun kakkabo jirage 12 kan tsibirin Cremea, sannan wasu 6 kan lardin Cresondor sannan biyu a kan Rustufm sau guda a kan jumhuriyar Adigyo, wani guda kuma a kan tabkin ruwa na Ozoof.

Kafin haka dai gwamnan lardin Kharson ya bada sanarwan a safiyar ranar Alhamis kan cewa jiragen yakin Ukraine wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kashe mutane 24 sannan wasu kimani 50 sun ji rauni a harin da suka kai kan wani otel ko masaukin baki a lardin.

A wani rahoton da sojojin kasar suka mikawa fadar shugaban kasa a  cikin sabuwar shekara, ya nuna cewa sojojin Rasha sun mamaye kasa mai fadin kilomita murabba;ii 6, 460 na makiya a shekara da ta 2025 da ta gabata, tare da garuruwa 334, rahoton yace sojojin Rasha suna samun ci gaba a yakin da suke fafatawa da kasar Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted