Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya

Ministan harkokin wajen Habasha Gideon Timotheos ya ce ya tattauna da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov kan batutuwa daban-daban da suka Shafi dangantaka tsakanin

Ministan harkokin wajen Habasha Gideon Timotheos ya ce ya tattauna da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov kan batutuwa daban-daban da suka Shafi dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma yadda za a kara inganta su.

Timotheos ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai bayan tattaunawar da ministocin biyu suka yi a ranar jiya  Talata, inda ya ce, “A yau mun tattauna kan yadda za a gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin a fannin nukiliya, da kuma a fannonin zuba jari, binciken kimiyya, da musayar al’adu.”

Ya kara da cewa, “Ciniki tsakanin kasashen biyu yana karuwa, amma idan aka kwatanta da damar da kasashen biyu suke da ita,  akwai abubuwa da dama da ya kamata a kara ingantawa da kuma habaka su”

Lavrov da Timotheos sun gana a watan Afrilu a Brazil a gefen taron ministocin BRICS, kafin jami’in na Habasha ya ziyarci Rasha a watan Satumba, inda shi da shugaban kamfanin Rosatom Alexei Likhachev suka rattaba hannu kan wani shirin aikin hadin gwiwa  tare da kamfanin samar da wutar lantarki na Habasha domin gudanar  da aikin tashar makamashin nukiliya ta Habasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments