Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito a jiya Litinin cewa an dakile wani yunkurin kisan gilla kan sakataren majalisar tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu a makabartar Troyekurov da ke birnin Moscow.
Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito majiyoyi suna bayyana cewa wadanda suka aikata laifin sun yi yunkurin tayar da bam ne a lokacin ziyarar Shoigu a kaburburan ‘yan uwansa.
Kazalika majiyoyin sun tabbatar da kame dukkan wadanda ake zargin tare da dakile shirin nasu, kamar yadda kafafen yada labaran Rasha suka rawaito.
Shoigu ya taba rike mukamin ministan tsaron kasar Rasha daga shekara ta 2012 zuwa 2014 kafin shugaba Vladimir Putin ya nada shi sakataren kwamitin tsaron kasar ta Rasha, wanda ya zama babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasar baki daya.