Ranar Kudus: al’ummar Iran zasu nuna hadin kan su ga duniya_ Pezeshkian

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu.

Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.”

Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar karshe ta azumin watan Ramadan domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu.

Ta kasance wani gangami na duniya ga musulmi da masu neman ‘yanci a wajen bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falastinu tare da yin Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa yankunan Falastinawa da kuma cin zarafin da take yi wa masallacin Kudus.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments