Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar.
A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka.
Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da yin sanadin salwantar rayukan fararen hula da basu bas u gani ba, in ji Cora Morris, jami’a a cibiyar sanya ido kan amfani da makamai ba bisa ka’ida ba da ke da mazauni a Burtaniya..
An tabbatar da cewa jirage marasa matuka masu dauke da makamai sun kashe fararen hula a kasashen Afirka masu yawa sakamakon tashe-tashen hankula, da hakan ya hada da kasashen Sudan, Somalia, Nigeria, Mali, Burkina Faso, da Habasha, inda akasarin hare-hare sun faruwa ne a wadannan yankuna.