Rahoto : Amurka Na Matsin Lamba Wa Ukraine Ta Gudanar Da Zabe Zuwa Karshen Shekara

Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da

Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow.

Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Ukraine da aka dakatar a yakin da ake yi da Rasha, suna bukatar a gduanar da su.

“Yawancin kasashen dimokuradiyya suna gudanar da zabe a lokacin yakinsu. Ina ganin yana da mahimmanci su yi haka,”in ji Kellogg.

Kamfanin dillancin labaran reuters ma ya rawaito wasu jami’an fadar White House sun tattauna batun matsawa Ukraine ta amince da gudanar da zabe a wani bangare na duk wata yarjejeniya ta farko da Rasha.

Trump da Kellogg sun ce suna aiki kan wani shiri na shiga tsakani a cikin watannin farko na sabuwar gwamnatin Amurka don kawo karshen yakin da ya barke a watan Fabrairun 2022.

Har yanzu dai ba a fayyace shirin ba kuma har yanzu ba a san yadda za a karbi shirin a cikin kasar Ukraine domin kawo karshen rikicin mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

A baya shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce Kiev za ta iya gudanar da zabe a wannan shekara idan fadan ya kare da kuma samar da kwakkwaran tabbacin tsaro ga Ukraine.

A cikin shekarar 2024 ne wa’adin shekaru biyar na Zelensky ya kamata ya kare amma ba’a iya gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a karkashin dokar soja ba, wanda Ukraine ta sanya a watan Fabrairun 2022.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments