Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan dukkanin cibiyoyin nukiliyar Isra’ila.
Jakadan dindindin na Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Jasem Yacoub al-Hammadi, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce “Al-Hammadi ya jaddada bukatar kasashen duniya da cibiyoyinta su tabbatar da alkawurran da suka dauka a karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD, da babban taron MDD, da hukumar IAEA da kuma taron bitar NPT na shekarar 1995, wanda daga bisani ya bukaci Isra’ila da ta mika dukkanin cibiyoyinta na nukiliya ga tsarin kiyaye zaman lafiya na IAEA.”
Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta ce jakadan Qatar ya yi kira da a kara kaimi ga kokarin da kasashen duniya ke yi na shigar da Isra’ila cikin tsarin NPT.
Sanarwar ta kara da cewa, dukkan kasashen Gabas ta Tsakiya, in ban da gwamnatin Isra’ila, suna cikin yarjejeniyar NPT, ta hana yadfuwar makamman nukiliya.
An dai bayyana cewa Isra’ila tana da manyan makaman nukiliya tsakanin 200 zuwa 400 a ma’ajiyar makamanta, wanda hakan ya sa ta kasance kasa daya tilo mai mallakar makaman nukiliya a yammacin Asiya.