Shugaba Vladimir Putin ya ce kasashen Yamma sun amincewa Kiev ta yi amfani da makamai masu cin dogon zango domin kai hari a kan Rasha, na nufin NATO za ta yi yaki da Rasha.
Putin ya yi magana ne a yayin da manyan jami’an diflomasiyyar Amurka da Birtaniya ke tattaunawa kan sassauta dokokin harba makaman kasashen yammacin Turai a cikin Rasha, wanda Kiev ke nema yau sama da shekaru biyu da rabi a yakin.
Putin ya shaidawa wani wakilin gidan talabijin na kasar cewa, “Wannan zai iya canza yanayin rikicin.”
Ya kara da cewa, “Yana nufin kasashen NATO, Amurka, kasashen Turai, zasu yaki da Rasha.”
‘’Bisa la’akari da sauyin yanayin rikicin, za mu dauki matakan da suka dace bisa barazanar da za mu fuskanta.”inji Putin.
Kalaman na Putin sun zo ne a daidai lokacin da Kiev ta matsa wa kasashen Yamma lamba da su samar da karin makamai masu karfi, yayin da Rasha ke ci gaba da kutsawa gabashin Ukraine.