Jakadan kasar Iran a birnin Moscow ya bayyana cewa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai kai ziyara kasar Rasha a wata mai zuwa domin rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan ci gaban manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.
Da yake magana a wani taro da daliban Iran a St. Petersburg, Kazem Jalali ya ce, Iran da Rasha a shirye suke su sanya hannu kan yarjejeniyar.
“Shugaban Iran zai tafi Rasha a ranar 17 ga watan Janairu, kuma yayin ziyarar Pezeshkian da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu,” in ji shi.
A shekara ta 2001, Tehran da Moscow sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dogon lokaci. Da farko an sanya wa’adinta na tsawon shekaru 10 amma an tsawaita shi har zuwa 2026.
Yanzu hakan dai kasashen biyu suna yin shiri na karshe don cika yarjejeniyar hadin gwiwa, wacce za ta iya tantance alakar da ke tsakaninsu a dukkan fannoni na shekaru 20 masu zuwa.
Har ila yau, a nasa jawabin, wakilin na Iran ya bayyana muhimmancin ayyukan tattalin arziki da suka hada da hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa, da kuma aikin shimfida bututun iskar gas na kasar Rasha zuwa Iran.
Jalali ya ci gaba da cewa kasancewar ‘yan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu na Iran a kasar Rasha zai taimaka wajen bunkasa dangantakar tattalin arziki.
Iran da Rasha dukkansu suna fuskantar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba musu ba bisa ka’ida ba, sannan kuma a cikin shekarun nan sun kara zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban.