Pezeshkian ya jaddada cikakken goyon bayan ga gwagwarmayar Palasdinawa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa ba tare da wani sharadi ba ga gwagwarmayar Palasdinawa, a yakin da suke yi da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa ba tare da wani sharadi ba ga gwagwarmayar Palasdinawa, a yakin da suke yi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a cikin wani sako a yayin taron kasa da kasa karo na 9 mai taken “Mujahid a gudun hijira” wanda aka gudanar a birnin Damghan na kasar Iran a lardin Semnan da ke arewacin kasar a wannan  Talata, tare da halartar baki daga kasashen musulmi daban-daban da jami’an kasa da na larduna. .

“A cikin kusan rabin karni, daga cikin abin da Jamhuriyar Musulunci ta sanya Iran ta sa a gaba, har da tabbatar da adalci da kare hakkin bil’adama a duniya, da kuma bayar da cikakken goyon baya ga gwagwarmayar da al’ummar Palastinu da ake zalunta ke yi da gwamnatin  Sahayoniyya.” inji Pezeshkian.

Shugaban ya ce tun farkon wa’adinsa ya bayyana cikakken goyon bayansa ga al’ummar Palastinu da wadanda ake zalunta a duniya.

Ya kuma ce gwamnatin Iran ta 14 za ta ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar Palastinawa kamar yadda gwamnatocin da suka gabata suka yi.

“Na yi imanin cewa, ya kamata mu dauki kanmu a kodayaushe wajen neman adalci da goyon bayan masu neman ‘yanci da kuma wadanda ake zalunta a kowane hali, domin neman adalci. In ji shi

Pezeshkian ya kara yabawa marigayi ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian a matsayin “fitaccen jami’in diflomasiyya mai himma da kwazo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments