Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce akwai bukatar musulmi su samar da hadin kai domin kare mutuncinsu da al’ummominsu.
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron makon hadin kan kasashen musulmi na kasa da kasa karo na 38, wanda aka bude jiya Alhamis a birnin Tehran tare da halartar malamai daga mazhabi Shi’a da na Sunna fiye da 144 daga kasashe 36.
Ya ce makiya suna haifar da sabani a tsakanin al’ummar musulmi, wanda ba za a iya samun nasara ba sai ta hanyar hadin kai.
“Hadin kai karfafa ikon Musulmai,” in ji Pezeshkian.
Ya kuma yi Allah wadai da rashin daukar matakin da kasashen musulmi suke yi dangane da laifukan da Isra’ila ke yi wa al’ummar Falastinu da kuma lalata asibitoci da masallatai da gwamnatin kasar ta yi.
“Isra’ila na aikata laifuka ne saboda mu (Musulmi) ba mu da matsaya da murya daya,” in ji Pezeshkian.
Shugaban na Iran ya jaddada cewa wajibi ne al’ummar musulmi su yi imani da hadin kai tare da tabbatar da hakan a aikace.
Ya yi gargadin cewa duk wani rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi tamkar tafiya ne a gefen wuta, ya kuma ce babu wani karfi da zai iya tunkarar al’ummar musulmi matukar suka samar da hadin kai.