Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ko a jikinmu a wanda ya ci zabe a Amurka.
‘’ba wani banbanci da wanda ya ci zabe’’ Iran ta dogare ne da manufofinta na cikin gida domin ci gaba inji shi.
Dama kafin hakan Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeili Baghaei ya fada a wannan Alhamis cewa Iran za ta yi wa sabuwar gwamnatin Amurka hukunce ne bisa manufofinta da tsarinta bayan da Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Laraba.
Mr Baghaei ya fada a wannan Alhamis cewa nasarar da Trump ya samu wata dama ce ga Amurka ta sake yin nazari kan munanan manufofinta a baya.
A shekarar 2018 ne Amurka, karkashin Shugaba Trump, ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla da Iran a shekarar 2015, sannan ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci takunkumai masu tsauri.
Baghaei ya sake jaddada matsayin Iran a baya na cewa sakamakon zaben Amurka ba shi da wani tasiri ga Jamhuriyar Musulunci.
“Zaben shugaban Amurka nauyi ne da ya rataya a wuyan al’ummar kasar, kuma a yanzu jama’ar Amurka sun zabi nasu zabi,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Abin da ke da muhimmanci ga Iran shi ne ayyukan da gwamnatin Amurka zata gudanar wanda zasu kasancewa Iran a matsayin ma’auni.”
Ko a ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta shaida wa manema labarai a Tehran cewa Iran ba ta ga wani bambanci tsakanin Trump da abokiyar takararsa ta jam’iyyar Democrat Kamala Harris ba.