Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa kasarsa bata neman yaki, kuma tana daukar tsaron yankin a matsayin na dukkan musulmi”.
Shugaba Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Sarkin Qatar a jiya Laraba a birnin Doha, inda ya bayyana cewa: “A gare mu tsaron yankin shi ne na dukkan musulmi”.
Massoud Pezeshkian ya ce “Tun da na hau kan karagar mulkin Iran, na bayyana cewa muna neman zaman lafiya da kwanciyar hankali, domin babu wata kasa ko yanki da za ta ci gaba a yaki.”
A game da hare-haren da Iran ta kai wa Isra’ila, Shugaban na Iran ya sake jaddada cewa Isra’ilar ce ta tilasta masu mayar da martani.
Da yake bayyana cewa Isra’ila ta kashe babban bakon Iran a Tehran a ranar rantsar da shi, Pezeshkian ya ce : “kawayen Isra’ila sun roki a kai zuciya nesa a rungumi zaman lafiya, kada mu mayar da martini, amma maimakon su daina kashe-kashen, wadannan yahudawan sahyoniya sun kara kaimi wajen kai hare-hare a Gaza da Lebanon. »
‘’Idan muka nuna halin ko in kula ga abin da Isra’ila ke yi, za ta ci gaba da yada hargitsi a yankin.
Shugaban ya jaddada cewa: “Isra’ila ta aikata laifukan da babu wani mahaluki da ya taba aikatawa a tarihi, wanda ya tilasta masu mayar da martini, kuma idan har Isra’ila ta dauki wannan hanya, za mu mayar da martini mai zafi. »
“Manufofin gwamnatin Sahayoniya shi ne yada rikici a yankin, wanda Dole ne mu hana rikicin,” inji Pezeshkian.