Pezeshkian: Rikici a gabas ta tsakiya babbar illa ce ga duniya baki daya

Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa

Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa.

Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran  a matsayin tushen rashin tsaro a yankin.

Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba neman kera makaman nukiliya ba.

Shugaba Pezeshkian ya ce Iran ta ba da hadin kai kuma za ta ci gaba da hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA domin kara tabbatar wa duniya da cewa shirinta na ayyukan farar hula ne, sabanin abin da makiyanta suke yadawa..

A nasa bangaren Firaministan Norway ya ce, kasarsa a shirye take ta ba da duk wani taimako da nufin warware matsalolin da ke faruwa a yankin yammacin Asiya a cikin lumana, tare da kara karfafa alakarta da kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments