Paparoma Leo 14 wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Lebanon ya gana da shugaban kasar Lebanon Josept Aun da kuma manya-manyan malamai da shuwagabannin kungiyoyin yan siyasa a kasar Lebanon.
A jawabin da ya gabatar a gaban wadannan shuwagabannin kasar Lebanon Lio na 14 ya bukaci, su rungumi zaman tare da kuma hakuri wajen hada kai da kuma gina kasar Lebanon.
Lio 14 ya ce mutanen kasar Lebanon sun sha wahala a tarihin kasar na zama, amma saboda gwazon da suke da shi wannan bai hana su zaman lafiya da juna ba. Wannan bai hanasu ci gaba da rayuwa ba. Duk da cewa akwai barazana mai yawa da ke fuskantar kasar.
Yace, zama tare da wadanda kuke da sabani a Akida da kuma kungiyoyin da basa dasawa da juna ba karamin jarrabawa ce ga mutanen kasar Lebanon kuma sun ci jarrabawar.
Kafin haka dai Paparoma Lio ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Turkiyya.***