Search
Close this search box.

Pakistan ta yi watsi da zargin gudanar ayyukan soji na sirri tsakaninta da Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi watsi da rahoton da wata kafar yada labarai ta Isra’ila ta fitar “marasa tushe”, tana mai cewa wani

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi watsi da rahoton da wata kafar yada labarai ta Isra’ila ta fitar “marasa tushe”, tana mai cewa wani yunkuri ne na “dagula ra’ayin jama’a da bayanan karya.”

Da take jawabi a taronta na mako-mako, Mumtaz Zahra ta soki rahoton jaridar Jerusalem Post, inda ta bayyana shi a matsayin “labarai na karya” tare da yin hakan domin cimma wasu manufofi a wannan lokaci mai mahimmanci.

Jaridar Isra’ila, ta yi iƙirarin cewa, idan rikicin soji ya barke  tsakanin Iran da Isra’ila, Pakistan za ta ba wa Iran makamai masu linzami masu cin dogon zango.

Zahra ta yi watsi da wadannan zarge-zargen kuma ta kara da cewa Pakistan ba ta da wani shiri kan hakan.

Bugu da kari, Zahra ta ambaci wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a baya-bayan nan tsakanin jami’an Pakistan da mukaddashin ministan harkokin wajen Iran bayan kisan gillar da aka yi wa Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na Hamas, inda Pakistan ta yi Allah wadai da zaluncin Isra’ila.

Tawagar Pakistan ta halarci wani taro na musamman na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah, bisa bukatar kasashen Iran da Falasdinu bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh a makon jiya.

A yayin taron an yi Allah wadai da keta hurumin kasar Iran da kuma yankinta, tare da wuce gona da iri da Isra’ila ke yi, kuma kasashen da suka halarci taron sun nuna goyon bayansu ga Iran da Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments