Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450.
Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin.
Gwajin makamin na sojojin Pakistan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakaninta da kasar Indiya, bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Kashmir.
A ranar 22 ga watan Afrilu ne dai aka kai wani hari akan masu yawon bude ido a yankin na Kashmir wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 26. Da akwai fargabar cewar kasashen biyu za su tsunduma cikin wani sabon yaki,bayan da Indiya ta zargi Pakistan da cewa tana da hannun a wancan harin.
Pakistan dai ta kore cewa tana da hannu, tare da yin kira ga Indiya da ta kaucewa tsokana, domin za ta mayar da martanin da ya dace gwargwadon harin da za ta kai mata.
Mahukuntan kasar Pakistan sun gargadi Indiya akan cewa, su kwana da sanin cewa; Islamabad tana da makaman Nukiliya.
A yau Asabar an yi musayar wuta a tsakanin sojojin kasashen biyu a tsawon yankin da ya raba su a yankin Kashmir.
A jiya Juma’a mahukunta a yakin Kashmir sun yi kira ga mazauna yankin da su tanadi abincin da zai ishe su na tsawon watanni biyu,saboda tsoron yiyuwar barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu masu karfin Nukiliya.