Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan
Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis.
Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul.
Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kawo yanzu ba a samu hasarar rayuka ba.”
Majiyar leken asirin Afganistan ta shaidawa Al-Araby Al-Jadeed cewa: Shugaban Taliban na Pakistan kuma wani babban kwamandan kungiyar ya tsallake rijiya da baya a harin da Pakistan ta kai kan Kabul.
A halin da ake ciki, wasu kafafen yada labaran Afghanistan sun sanar a cikin wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba, y ace: An kashe Mufti Noor Wali Mehsud shugaban Taliban na Pakistan a wani hari da aka kai ta sama a Kabul a daren yau.