Pakisatan Ta Maida Martanin Farmakin Sindoor Na Indiya Kan Rumbun Makamai Masu Linzami Na Indiya

Gwamnatin kasar Pakisatan ta basa sanarwan kai hare-haren maida martani kan kasar Indiya, inda tayi amfani da makamai masu linzami wadanda suka fada kan rumbun

Gwamnatin kasar Pakisatan ta basa sanarwan kai hare-haren maida martani kan kasar Indiya, inda tayi amfani da makamai masu linzami wadanda suka fada kan rumbun ajiyar makaman kasar ta Indiya da wani filin tashin jiragen.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar Nacewa daga wadannan wurare biyu ne makaman kasar Indiya suka tashi suka kuma yi sanadiyyar kashe mutane fararen hula a cikin kasar Pakisatan a makon da ya gabata.

Labarin ya kara da cewa sojojin Pakisatan sun bawa wannan farmakin maida martani suna [Bunyanun Marsus) inda suka dauki aron Kalmar daga wata ayar al-kur’ani mai girma.

Hare-haren maida martanin sun auku ne a safiyar yau Asabar, don haka har yanzun bamu ta bakin kasar Indiya ba.

Yaki a tsakanin kasashen biyu ya soma ne daga ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, inda kasar Indiya ta zargi Pakistan da hannu a cikin hare-haren da wasu yan ta’adda suka kai a yankin Pahalgam na yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar Indiya inda mutane 26 masu yawan shakatawa ko bude ido suka rasa rayukansu.

Ba tare da bata lokaci ba sojojin kasar Indiya suka fara cilla makamai kan kasar Pakistan, daga ciki har da farmakin da ta kira “sindoor”.

Da farko kasar Pakisatan ta musanta zargin ta kuma yi allawadai da hare-haren na ta’addanci a cikin kasar Indiya. Sai dai tunda kasar Indiya bata saurareta ba, bata da zabi in banda maida martani a safiyar yau Asabar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments