Nukiliya : Iran ta gargadi kasashen yamma akan daukar duk wani irin mataki kan ta

Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula

Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a mako mai zuwa.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya yi watsi da rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, yana mai gargadin daukar matakin da ya dace.

Kazem Gharibabadi ya yi wadannan kalamai ne, bayan da hukumar ta IAEA ta yi zargi a cikin wani rahotonta na sirri ga kasashe mambobinta cewa Iran ta gaza bayar da rahoton ayyukanta na nukiliya a wasu wurare uku da ba a bayyana ba, tare da bayyana damuwarta game da tarin uranium da ake zargin an wadatar da shi zuwa kashi 60 cikin dari.

Ya ce rahoton ya dogara ne kan “jerin bayanan karya da gwamnatin sahyoniya ta bayar” tun sama da shekaru ashirin.

Ya kara da cewa, an yi watsi da dukkan tuhume-tuhume kan ayyukan nukiliyar Iran da suka gabata a karkashin kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2231, wanda a hukumance ya amince da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Gharibabadi ya kuma lura cewa rahoton na hukumar ya sake nuna yadda IAEA ke siyasantar da ayyukanta a kan Iran.

Ya sake nanata cewa “Iran ba ta neman makaman nukiliya kuma ba ta da wani makaman nukiliya.” Kamar yadda ake ta yayatawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments