Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF).
Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar.
Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.”
Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa kungiyar.
To saidai dangankata ta yi tsami tsakanin faransa da sojojin dake mulki a kasashen guda uku a baya bayan nan.
Kungiyar ta OIF, “maimakon tallafawa wadannan kasashe wajen cimma manufofin raya al’ummarsu, (…) ta kauce wa hanya inda ta sanya siyasa a cikin lamuranta,” in ji ministocin harkokin wajen kawancen kasashen guda uku na Sahel a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a yammacin jiya Talata.
Kungiyar ta OIF, da ta hada kasashe da gwamnatoci 93, manufarta ita ce inganta harshen Faransanci da raya al’adu, don ƙarfafa zaman lafiya, da dimokuradiyya da ‘yancin dan adam, don tallafawa ilimi, horo da bincike, da kuma inganta hadin gwiwar tattalin arziki don samun ci gaba mai dorewa.
Sai nan da watanni shida masu zuwa ne ficewar kasashen za ta tabbata.