‘Yan sanda a birnin Abuja sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa Zanga-zangar masu neman a saki jagoran ‘yan awaren Biafar Nnamdi Kanu wanda ake yi wa shari’a bisa tuhumarsa da ayyukan ta’addanci.
Shi dai Kanu yana jagorantar kungiyar ‘yan asalin Biarafa ( Ipob) a takaice wacce a hukumance an haramta, saboda kiran da take yin a balle yankin kudu masu gabashin kasar da ‘yan kabilar Igbo suke da rinjaye domin kafa musu kasa mai cin gashin kanta.
Jami’an tsaro sun rika yin sintiri a tsakiyar birnin Abuja, da motoci masu silke da kuma masu watsa ruwan zafi. Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan masu goyon bayan kungiyar da su ka yi kokarin taruwa.
Bugu da kari, an ga wani adadi na sojoji suna taimakawa ‘yan sandan a kokarin tarwatsa masu Zanga-zangar.
Shi dai Kanu ana tsare da shi ne tun a 2021, da hakan ya sa masu goyon bayansa suke yin kira da a sake shi, da kuma yin watsi da zargin aikin ta’addanci da ake yi masa. Kanu dai ya sha kore tuhume-tuhumnen da ake yi masa a duk lokacin da aka gabatar da shi a gaban kotu.
Nigeria ta yi yakin Basasa na tsawon shekaru 3 da ya fara a 1967, wanda kuma ya ci rayukan fiye da mutane miliyan daya.