Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta sanar da cewa ta kwato mutane 23 da masu garkuwa da mutane su ka kama a cikin dajin Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ya sanar a jiya Lahadi cewa sun kwato mutanan ne a ranar 2 ga watan Febrairu, 2025.
Jami’in ‘yan sandan ya ce sun sami nasarar kwato mutanan ne bayan da su ka sami bayanai na sirri akan kai da komowar masu garkuwa da mutanen.
Haka nan kuma Hassan ya ce, an yi taho mu gama ne da masu garkuwa da mutanen a kusa da kauyen Doka dake karamar hukumar ta Kajuru.
Barayin suna kokarin sauya wa mutanen da su ka yi garkuwa da su, wuri ne a lokacin da ‘yan sandan su ka rutsa da su.
A yayin bata-kashin jami’an tsaro da su ka kunshi ‘yan sanda da kuma sojoji sun kashe barayin masu yawa da kuma tilastawa wadanda su ka saura a raye, janyewa cikin daji.