Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa

Ma’aikatar harkokin wajen Njgeria ta sanar da bai wa dan takarar shugabanncin  kasar Guinea Bissau, Fernando Dias da Costa, ya kuma tsaya takara ne a

Ma’aikatar harkokin wajen Njgeria ta sanar da bai wa dan takarar shugabanncin  kasar Guinea Bissau, Fernando Dias da Costa, ya kuma tsaya takara ne a tare da shugaban kasar  Umar Sisoko  Embalo da sojoji su ka kifar da gwamnatinsa kwanaki kadan bayan zabe.

A ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai Dias Da Costa ya sanar da cewa,shi ne wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, tare da zargin Embalo da cewa shi ne ya shirya juyin mulkin da ya kawo karshen zaben kasar, tun kafin a sanar da sakamakon zaben.

Haka nan kuma ya ce ya tsallake rijiya daga kokarin kama shi a ranar da aka yi jiyin Mulki, ya kuma boye, har sai da ya sami goyon bayan kasar Najeriya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, al-Kassim Abdulkadir ya ce; manufar bayar da mafakar siyasar, shi ne kokarin hana dambaruwar siyasar a cikin kasar ta Guinea Bissau da rashin zaman lafiya a cikin yammacin Afirka.

Shi kuwa shugaban kasar da aka hambarar Embalo an tsare shi na wani lokaci, sai dai kuma an sake, shi sannan kuma ya nufi kasar Senegal domin samun mafakar siyasa. Sakin Embalo ya biyo bayan tsoma bakin kungiyar tarayyar Afirka ne wacce ta yi Allawadai da juyin Mulki.

Kungiyar ta Ecowas ta aike da tawaga zuwa kasar ta Guine Bissau inda su ka gana da sojojin da su ka yi juyin Mulki. Ministan harkokin wajen Saliyo Thimothy Musa Kaba wanda ya jagoranci tawagar ya ce; Tattaunawar ta haifar da Da,mai ido. Sai dai kuma ta jadda kin amincea da juyin Mulki, tare da yin kira da a koma aiki da tsarin Mulki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments