Nigeria: Mutane Da Yawa Sun  Rasa Rayukansu Sanadiyyar Harin Makiyaya A Jihar Benue

 Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42. Mahukunta

 Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42.

Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane 10 a kauyukan Tyolaha, Tse-Ubiam, kamar yadda shugaban karamar hukuma   Gwer ta yamma Victor Omnin ya bayyana.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana wa ‘yan jarida abinda ya faru da cewa; na takaici ne, domin a wannan lokacin da muke Magana ana ci gaba da gano gawawwaki.”

Jahar Benue tana tsakiyar kasar Nigeria ne a yankin da ake kira : Middle-Belt”. An kuma dauki shekaru masu tsawo ana riciki a tsakanin makiyaya da manoma akan kasa saboda rushewar tsarin burtali.

Ofishin Gwamnan jihar ta Benue Hyacinth Lormem Alia, ya kuma sanar da cewa daga cikin wadanda aka  kai wa hari da akwai malamin addinin kirista,amma yana a raye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments