Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro

Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi

Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta

Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da makamai da suke karakaina a yankin.

Gwamnatin ta Kwara ta dauki wannan matakin ne bayan wani lokaci kadan daga kustawa cikin wata majama’a da masu dauke da makamai su ka yi a Eruku dake karamar hukumar Ekiti.

Mazauna yankin dai sun fada cikin frigici da razana hakanan kananan hukumomin da suke makwabtaka. An bayar da umarnin a rufe makarantun kwana na Irepodun saboda rahotanni na sirri da ake da su cewa za su iya zama wuri na gaba da za a kai wa hari.

Arewacin Najeriya dai yana fuskantar matsalolin tsaro da a farkon wannan makwan aka sace dalibai 25 a makarantrar Maga ta ‘yan mata a jihar Kebbi. A yayin harin da masu dauke da makamai su ka kai sun kashe malami da kuma mai gadi.

A Jahar ta Kwara mahukunta sun ce ba za a bude makarantun ba har sai idan jami’an tsaro sun sanar da samun yanayin da ya dace a yi hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments