Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata.
Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar.
Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi aiki tukuru domin magance yawan hatsurran da ake samu na jiragen ruwa a cikin gida wanda yake haddasa asarar rayuka da dama.
A Nigeria dai ana yawan samun hatsarin kananan jiragen ruwa masu jigilar mutane musamman ma dai a cikin arewacin kasar, da hakan yake haddasa asarar rayuka da yawa. Cunkoson mutanen da suke hawa knanan jiragen da kuma rashin rigunan tsira idan hatsari ya faru, suna cikin dalilin asarar rayuwa masu yawa da ake samu. Haka nan kuma karancin masu ceto mutane da za su zama aikinsu kenan a gabar ruwa, idan aka sami bullar hatsurra.