Netanyahu Ya Dage Kan Samun Nasara A Yakin Gaza Amma Abinda Yake Kasa Akasin Haka

A gobe Talata ce 7 ga watan Otoba, yakin tufanul-Aksa ya ke cika shekaru 2 tsakanin HKI da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin

A gobe Talata ce 7 ga watan Otoba, yakin tufanul-Aksa ya ke cika shekaru 2 tsakanin HKI da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Jaridar ‘The National’ na kasar Amurka ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa gwamnatinsa tana samun nasara a yakin, duk da cewa abinda yake kasa yana nuna akasin haka. Musamman idan an dubi manufofin HKI na fara shiga yakin.

Wasu masana a HKI basu amince da da cewa Natanyahu yana samun nasara a wannan yakin ba. Wanda shi ne yaki mafi tsawo wanda HKI ta shiga tun bayan kafata shekaru kimani 80 da suka gabaya.

Jaridar ‘The Nation’ ta yi hira da Nimrod Novik daya daga cikin yan tawagar tattaunawan gwamnatin HKI yana cewa a ganinsa HKI ta fadi a yakin 7 ga watan Octoba. Duk da cewa ma’aikatar leken asirin kasar ta sami nasarari a Lebanon,Siriya, da kuma Iran.

Jaridar ta kammala da cewa, ganin yadda HKI ta zama saniyar ware a duniya, da kuma gazawar Natanyahu wajen cimman manufofin shiga wannan yakin, mafi yawan yahudawan HKI basu amince da samun nasara a yakin kamar yadda Natanyahu  yake gani ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted