NBS: Hauhawar Farashi Ya Karu Zuwa Kashi 34.60 A Watan Nuwamba A Najeriya

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa, hauhawar farashi a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 34.60 a watan Nuwamban 2024. Wannan na nufin an

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa, hauhawar farashi a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 34.60 a watan Nuwamban 2024.

Wannan na nufin an samu karin 0.72 daga kashi 33.88 da aka samu a watan Oktoban 2024.

Idan aka kwatanta da watan Nuwamban 2023, lokacin da hauhawar farashi ya kasance 28.20, a wannan shekarar an samu ƙarin 6.40.

Rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyaki sun tashi sosai a Nuwamba 2024, idan aka kwatanta da watan Nuwamban 2023.

Duk da haka, idan aka duba hauhawar farashin a kowane wata, hauhawar farashin a Nuwamba 2024 (2.638) ya yi kasa kadan da wanda aka samu a watan Oktoba 2024 (2.640).

Hauhawar farashin kayan abinci ya tashi zuwa 39.93

Hauhawar farashin kayan abinci ya tashi, wanda hakan ke nuni da kayan sun yi tsada zuwa kashi 39.93 a watan Nuwamba 2024, daga 32.84 a watan Nuwamba 2023.

Wannan karin ya shafi kayayyakin kamar su ayaba, masara, shinkafa, manja, da man gyada.

A kowane wata, farashin kayan abinci yna tashi da kashi 2.98 a watan Nuwamba 2024, wanda ya ƙaru kaɗan daga kashi 2.94 a watan Oktoba.

Kayayyakin da suka tashi sun hada da kifi, shinkafa, ayaba, madara, madarar shanu, nama, kaza da sauransu.

Matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekara

Matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekaru 12 wanda ya kare a watan Nuwamba 2024 ya kai kashi 38.67.

Wannan na nufin an samu karin kashi 11.58 idan aka kwatanta da matsakaicin hauhawar da aka samu a cikin shekarun 12 da suka gabata, wanda ya kasance 27.09 a watan Nuwamban 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments