A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia.
Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Estonia ta bayyana abinda ya faru da cewa, keta hurumin kasar ne a fili, wanda kuma ya sa kungiyar ta Nato ta yi kakkausar suka, tare da bayyan shi a matsayin tsokana daga Rasha.
Rasha dai tana zaman tsami da kungiyar Nato saboda yakin kasar Ukrainiya wanda ya shiga cikin shekaru na 3 ana yi.
A gefe daya Nato tana ci gaba da aike wa da sojojinta zuwa kasar Poland wacce take makwabtaka da Ukiraniya, bayan da ita ma ta zargi Rashan da cewa ta keta hurumin sararin samaniyarta.