Natanyahu Ya Bada Umurnin A Dakatar Da Musayar Fursinoni Da Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya A Gaza

Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane

Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau.

Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza.  Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da kuma zuwa lokacinda za’a samarwa ma’aikatansa tsaro a gaza.

Kafin haka dai falasdinawa suna son musayar fursinonin yahudawa kimani 100 da suke hannunsu da faladinawa 2000 wadanda suke hannun HKI.

A yau Alhamis dai Falasdinawa sun saki wata fursina guda, ba yahudiya, sannan tana saran a saki falasdunawa 110 30 daga cikinsu yara kanana.

Ya zuwa yanzu dai yahudawan sun janye sojojinsu daga yankunan Falasdinawa da dama a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments