Natanyahu Ya Amince Da Kissan Masana Fasahar Nukliya Na Kasar Iran

Benyamin Natanyahu firai ministan HKI ya amince da cewa gwamnatinsa ta kashe masana fasahar Nukliya na kasar Iran da dama, don haka kasar ci gaba

Benyamin Natanyahu firai ministan HKI ya amince da cewa gwamnatinsa ta kashe masana fasahar Nukliya na kasar Iran da dama, don haka kasar ci gaba a wannan bangaren.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Amurka mai sun a FOX NEWS. Wannan ikrarin dai ya fidda shakka da ake da shi ne cewa gwamnatin HKI ce take kashe masana fasahar Nikliyar kasar kuma wannan furucin ya zama shaida a kansa a duk lokacinda al-amarin ya zaman a shari’a.

Har’ila yau furucin ya tabbatar da cewa HKI tana zagon kasa wa JMI wacce shirin makamashin nukliyar ta, ta zaman lafiya ce karkashin kula na hukumar IAEA.

Banda haka wannan ya tabbatar da cewa gwamnatin HKI gwamnatin yan ta’adda ce, wacce take kokarin hana zaman lafiya a yankin Asia ta yamma.

Natanyahu ya fadawa FOX NEWS kan cewa, HKI ta sha kishe masana fasahar Nukliya na kasar Iran, amma wadanda ta kashe a yakin kwanaki 12 sun fi sauran daraja a wajensa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted