A wajen taron jana’izar mahaifiyarsa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa, laifin yaki yaki da aka aikata a Rafah ya kawar da duk wani dalili na karya yana mai cewa: Wajibi ne wannan laifin ya farkar da dukkan mutane da suka yi a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ahed cewa, Sayyid Hassan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: “Ban samu damar halartar jana’izar mahaifiyata da ta rasu ba. Wajibi na ne in kasance a gaba, amma yanayin tsaro ya hana ni yin hakan.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi tsokaci kan laifukan baya-bayan nan da gwamnatin sahyoniyawa ta aikata a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza inda ya ce: Kisan kiyashin na Rafah ya nuna irin zaluncin da makiya suke aikatawa da mummunan kudirin da suke da shi.
” Muna fuskantar abokan gaba da ba su yarda da kowace ɗabi’a ko ‘yan adamtaka ba, sun fi na ‘yan Nazi muni. Mummunan laifin da suka aikata na Rafah ya kamata ya farkar da duk wani lamiri na masu yin shuru da nuna halin ko in kula a duniya kana bin da yake faruwa a Gaza.
Nasrallah ya ci gaba da cewa: Laifin Rafah ya kawar da duk wani abin da ake rufa-rufa a kansa da kirkiro dalilai na karya domin kare Isra’ila.