Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar

Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar.

A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne.

Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar.

Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya,”, inda ya kara da cewa ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar.

“Saboda haka ya ayyana Najeriya kasar da ake da damuwa a kanta.”

Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa ‘yan majalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments