Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa a kai shi ne yadda za su hada kai wajen magance matsalolin tsaro don amfanin duniya.
A farkon watan Nuwamban nan Trump ya ce ya bai wa ma’aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za ta kai hari Najeriyar. Sai dai ministan ya ce ba ya tunanin Amurka za ta yi hakan, ” muna ci gaba da tattaunawa, kuma ana samun ci gaba a tattaunawar, mun wuce nan yanzu”.
Trump ya ce addinin Kirista na fuskantar barazana a kasar da ke yammacin Afirka, Ya kuma yi gargaɗin cewa idan Najeriya ba ta kawo karshen kashe kashen ba, Amurka za ta kai hari.
Akan samu hare-hare da rikice-rikice da dama da kan shafi dukkanin bangarorin biyu kristoci da musulmi .