Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan gano wasu daga cikin wadanda suke daukar nauyin zanga zangar tsadar rayuwa a kasar daga kasashen waje, kuma har ta sanya su cikin jerin sunayen wadanda ake nema, kuma da zaran sun shigo kasar za’a kamasu a mikawa hukumomin da suka dace.
Banda haka labarin ya kara da cewa, an rufe asusun ajiyarsu ta kudadensu na Najeriya.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban hukumar shige da fice ta kasar Kemi Nandap tana fadar haka, ta kuma kara da cewa, hukumarta ta kara yawan ma’aikatanta a kan iyakokin kasar na sama da kasa da ruwa don tabbatar da cewa an gano duk wanda ya shigo kasar daga cikinsu.
Ms Nandap ta bayyana haka ne a jiya talata bayan taron manya manyan jami’an tsaron kasar wanda ya hada da babban hafsan sojojin kasar Christopha Musa a helkwatan sojojin kasar a Abuja.
Daga karshen shugabar hukumar shige da fice ta kasar, ta ce hukumarta tana aiki don ganin kasashen waje basu yi shishigi cikin abinda yake faruwa a kasar ba.
Sannan sipeto-janar na yansandan kasar Kayode Egbetokun ya fadawa wasu kafafen yada labarai kan cewa sun gano wasu wadanda suke daukar nauyin masu zanga zanga a kasar, yan Najeriya mazauna kasashen waje ne, amma bai yi wani Karin bayani ba.