Majalisar Zartarwa ta amince da daftarin Naira tiriliyan 47.9 a matsayin Kasafin Kuɗin Najeriya na 2025.
Ministan Kasafi da Tsare-Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila na daga cikin ƙusoshin gwamnati da suka halarci taron.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan Shugaba Tinubu ya soke taron Majalisar Zartarwa da aka shirya gudanarwa a ranar Larabar makon jiya.
Tinubu ya ɗage taron ne sakamakon mutuwar Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.