Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Ya Kafa Kwamitin Gano Dalilan Ballewar Madatsar Ruwa Ta Ala’u

Gwamnan jihar Borno a arewa maso gabacin tarayyar Najeriya Babagana Umar Zulum ya kafa kwamitin kwararru don gano musabbabin rushewar madatsar ruwa ta Ala’u wanda

Gwamnan jihar Borno a arewa maso gabacin tarayyar Najeriya Babagana Umar Zulum ya kafa kwamitin kwararru don gano musabbabin rushewar madatsar ruwa ta Ala’u wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a cikin birnin Maiduguri babban birnin Jihar Borno da kewaye a cikin watan da ya gabata.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto sakataren gwamnatin Jihar Alhaji Bukar Tijjani yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa ambaliyar ruwan ya mamaye birnin Maiduguri, kuma mutane kimani miliyon 2 ne suka kauracewa gidajensu sabo ambaliyar Ruwan. Sannan wasu da dama sun rasa rayukansu. Banda haka gidaje da dama da gine gine ne suka rushe.

Ambaliyan ruwa na watan Satumban da ya gabata dai yana daga cikin ambaliyan ruwa mafi muni da aka taba yi a tarihin jihar Borno.

Gwamnan yana bukatar sanin dalilan ballewar madatsar ruwa ta Alau ne don sanin matakan da zai dauka don ganin ba’a sake irin wannan ambaliyan ruwan ba. Da kuma fitar da sabbin hanyoyi masu aminci wadanda mutanen jihar zasu amfana da Ruwan madatsar Ruwan wajen ayyukan noman rani, da kuma samar da Ruwan sha ga birnin Maiduguri da kewaye.

Kwamitin wanda ya ya kunshi kwararru 26 yana da Injiniya Abba Garba a matsayin shugabansa. Kuma a yau ne gwamnan ya kaddamar da kwamitin a gidan gwamnatin don ya fara aikisa da gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments