Najeriya: Gwamna Sani Yace Biyan Kudaden Fansa Ko Ba Haka Bai Da Muhimmanci

Gwamna Uba Sanin a jihar Kaduna ya bayyana cewa batun ko an biya kudaden fansa ko kuma ba’a biya ba, bai da muhimanci , abu

Gwamna Uba Sanin a jihar Kaduna ya bayyana cewa batun ko an biya kudaden fansa ko kuma ba’a biya ba, bai da muhimanci , abu mai muhimmanci shi ne yara da kuma malaman da aka sace sun dawo gida ba tare da an cutar da suba.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Gwamna Uba Sani yana fadar haka a hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Chennel TV a jiya Lahadi. Ya kuma kara da cewa ya ji dadin an saki dukkan wadanda aka sat aba tare da an cutar da su ba.

A ranar 7 ga watan Maris ne wasu yan ta’adda suka sace dalibai da malamansu kimani 137 daga makarantar LEA Kuriga a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna suka shigha  da su daje suka kuma nemi kudaden fansa na naira biliyon guda kafin su sake su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments