Najeriya Da Ghana Sun Jaddada Aniyarrsu  Wajen Kara Fadada Alakarsu A Dukkanin Bangarori

Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun  tattauna batutuwa da dama domin  karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar

Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun  tattauna batutuwa da dama domin  karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka.

An gudanar da ganawar ne  a Abuja  bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da  halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban birnin Ghana.

Wannan dai ya zo ne watanni biyu bayan rantsar da Mahama bayan day a sake komawa kan karagar shugabancin kasar Ghana.

Daga cikin muhimman batutuwa da shugabannin kasashen na Najeriya da Ghana suka yi dubi a kansu, hard a yadda za a kara karfafa alakoki a dukkanin bangaroria  tsakanin kasashen biyu.

Baya ga haka kuma sun tabo batun rarrabuwar kawuna da aka samua  tsakanin mabobin kungiyar ECOWAS, da kuma matakan day a kamata a dauka domin dinke wannan baraka, da hakan ya hada hard a shiga tattaunawa da kasashen da suka balle suka kafa nasu kawancen, wato Nijar, Burkina Faso da kuma Mali, domin samun fahimtar juna da kuma yin aike tare domin ci gaban yankin da al’ummominsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments