Najeriya Ba Za Ta Karbi ‘Yan Ci Ranin Kasar Venezuela Da Amurka Za Ta Kora Ba

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin Amurka  mai suna Flavour Flav da ya shahara a shekarun baya, wajen mayarwa da shugaban Amurka Donald Trump martani da cewa: Babu abinda zai iya yi ma ka.”

Jaridar Wall Street Jouran ta buga labarin dake cewa; A yayin taron da aka yi a tsakanin wasu shugabannin kasashen Afirka biyar da shugaban kasar Amurka a fadar White House, an bijiro musu da karbar bakuncin ‘yan ci-ranin kasashe waje da Amurka take son kora daga cikinta.

Jaridar ta ambaci Nigeria a cikin kasashen da Amurka ta bijirowa da bukatar ta karbi bakuncin ‘yan ci-ranin kasar Venezuela su 300.

Ministan ya bayyana karbar bakuncin ‘yan ci-ranin a matsayin wani Karin nauyi akan kasar wacce take fama da nata yanayin na musamman.

Amurka ta yi barazanar karawa Najeriya kudin Fito na kayan kasuwanci idan ba ta amince ta karbi ‘yan ci-ranin ba, ko kuma a hana ‘yan kasar Visa ta shiga Amurka.

Sai dai ya ce; kasar a shirye take ta yi hulda da Amurka a cikin fagagen ma’adanai, iskar Gas da kasuwanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted