Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI.
A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar yaki, sai dai an bukace su da su dakata, domin bayar damar a dauki wasu matakai na daban.
Sheikh Na’im Kassim ya zargi Amurka da rashin daukar mataki akan HKI ta dakatar da keta yarjejeniyar da take yi, duk da cewa tana cikin masu sa ido akan tsagaita wutar.
Haka nan kuma ya yi ishara da komawar mutanen kudancin Lebanon zuwa garuruwa da gidajensu duk da harbinsu da sojojin mamaya suke yi.
Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, wanda duk yake da karama yake kuma jin daukaka a tare da shi, babu abinda zai tsorata shi, da hakan shi ne abinda ya faru.
Sheikh Na’ima ya kuma jinjinawa mahukuntan kasar Lebanon akan kin amincewa da bukatar Amurka na bar wa HKI damar kara tsawon wa’adin zamansu a kudancin Lebanon. Haka kuma ya dorawa Amurka da Faransa da MDD alhakin abinda zai biyo baya idan Isra’ilan ba ta janye ba.