Ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya a Abuja ta musanta zargin da cewa ana kishe kiristoci a kasar.
Jaridar Premium timnes ta Najeriya ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Jumma’a ta kuma kara da cewa rahotannin da suka yada wannan karaiyar sun son ingiza gwamnatin Amurka ta dauki Najeriya a cikin jerin kasashen da suke nuna bambanci a cikin mutanen kasashensu. Wanda ba hakaba.
A ranar laraban da ta gabata ce kwamiti mai kula da al-amuran Afirka a majalisar dokokin kasar ta bukace gwamnatin Amurka ta dauki mataki a kan Najeriya saboda abinda ya kira kissan kiristoci a Najeriya . Shugaban karamin kwamitin Chris Smith yayi kira ga shugaba Trump ya dorawa Najeriya takunkuman tattalin arziki masu tsanan kan wannan zargi